Shin bama shawarce ku zuwa ga abubuwa masu amfani ba?
Rayuwar mutane a kafafen sadarwa,za mu iya samun rabe-rabe na kalolin mutanen da suke rayuwa a cikinta.In mu ka biyo ta tsarin ilmi:
1.Akwai malamai,wadandan kowa ya san malamai ne duniya ta shaida.
2.Akwai dailban ilmi.
3. Akwai jahilai,wadanda sun san basu sani ba,dan haka duk wanda suka ga yana magana da ta shafi addini,walau yana daga cikin kashi na farko ko na biyu koko kura ce da fatar akuya masu suffofin beraye to duk suna kiran su malamai ne, kuma suna amanna da duk abunda sukaji daga wadannan mutane dari bisa dari(Abun tausayi)
4.Akwai yayyen jahilai masu kama da kannan shaidan,su basu sani ba,ba su kuma san cewa lallai fa basu san komai ba,dan haka suke ji a jikin su ma ai sun san komai basu bukatar sani(Murakkabai).
A yanzu kafafen sadarwa sun tumbatsa sun kuma yi cikar dammu,sannan cikin ikon Allah anyi kokarin samun ci gaba ta hanyar samar da hanyoyi na da'awah sosai,malaman da a farko suke fahimtar amfani da kafar bai dace ba suma sun fahimci duniyar ilmi tana kara ci gaba ne ga al'umma idan ya kasance suna amfani da ababen zamanin da suka dauke hankula kashi tamanin a cikin ta suma sun shigo ana damawa da su.
Sai dai abinda yake bamu tausayi ya ke kuma kona mana rai shine?
1. Akwai daga cikin malaman da abubuwan da suke fada ko suke rubutawa iyakarsa kan yatsun hannun su ko harsunan su. Za ka sami malami shine kan gaba wajen azalzala wutar gaba,habaici ko rikici bisa sabanin da asalin sa ba addinin ya shafa ba amma sai an dankwasa shi ta ko wane hali ya zama cikin addini,ina kiran su da MALUM -MALUM dan managarcin malami darajar shi tafi karfin gutsiri tsoma.
Dan haka yan'uwa masu neman ilmi a SN ayi hattara.
2.Akwai daga daliban ilmi,wadanda tun daga kalaman da suke rubutawa na raddi ma manyan su ko malamansu za ka fahimci ko ya girma irin wancan malamin za'ai na farko,domin a duk inda dalibin ilmi na kwarai yake zaka sameshi da abubuwa kamar haka.
1.Me girmamawa ne ga manyansa.
2.Me kyautatawa ne ga yan'uwan sa
3.Sannan me kyakkyawan nazari ne da bincike kafin yai magana a kan dukkan abunda ya san zai iya jawo mishi wata tawaya bisa siradin da yake kai na neman ilmi,amma yanzu daliban ilmi da yawansu ba sa bincike sai akan abunda yake na jayayya ne,me bata lokaci da nakasa dalibi ta hanyar kwashe albarkar karatun,ya kasance kullum in ka ji motsin shi to haushi yake bayan Allah ya karrama shi cikin jinsin yan Adam.
Jahilai,sune mutanen da na fi tausaya ma wa ta yadda suke sakin kwakwalen su ana ta gwarawa sun zama tamkar rakuma da akala su duk inda aka ja su tafiya su ke.Dan Allah!Dan Allah ba dan mu ba,ku taimakawa kawunan ku ku nemi ilmi a inda ya dace,kada ku biye ma ma'abota son zuciya a cikin addini su halakar da mu bayan sun san hanyoyin gyara rayuwar su.
Mu sami addinin mu na musulunci ba kara zube ya barmu ba,a cikin dukkan abubuwan da zami akwai ka'idoji na yin su.
Misalin Aure: Ba je mana akai da mutum ya balaga kuma yana da hankali ko kudin yi ba shike nan ai ta sambada mishi yaran mutane yana jerawa a gida ba,in anyi magana yace an fada mishi hadisi ne yaji Annabi yace ai aure a hayayyafa dan yayi alfahari da mu ranar alkiyama ba dan haka mata hudu zaiyi dan ya sami yaya hamsin.
Wallahi idan har me mata daya wanda ya cika sharuddan da addini ya tsara ya auri mace daya ya sami yaya biyu na gari wadanda suka hidimtawa addini sai annabi ya fi alfahari fiye da kai da za a sami hamsin wajen ka amma taron yuyu yuyu daga dan haram sai dan shege.Dan haka yana da kyau kaje malamin ka yai ma bayanin hadisin nan yadda ya kamata zamuyi farin cikin jin cewa bayan ka fahimci hadithin ne za ka fara kokarin aiki da shi.
Allah ka jikan mu ba dan halin mu ba ka kara jaddada imani a cikin zukatan mu.Ka bawa shugaban kasar mu da sauran musulmi lafiya ka kara kunyata maqiya.
Yan uwanku a musulunci
Marnaf Abubakar
&
Nabeelatu D Aleeyu
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve