Wednesday 15 February 2017

WA'AZIN JIHAR KATSINA NA GARIN DAURA, FEBRUARY, 2017.


A ranar Asabar ne 11 ga watan Fabrairu 2017, aka gabatar da gagarumin Wa'azin Jiha a garin Daura, Hedikwatar mulki ta Daura a jihar Katsina.
Garin Daura,  garine da yake da dunbin tahiri kala-kala, daga ciki akwai; tabbatuwa da kuma yaduwar Sunnah da Ahlus-Sunnah.
A garin Daura aka haifi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam, Sheikh Dr. Abdallah Saleh Pakistan daga nan ya fito, anan aka haifi babban Mahaddacin Al-Qur'anin nan Maigirma, mai jawa Sheikh Abdur-razaq Yahya Haifan baki a wurin Tafsirin Azumi a Abuja, kuma dai shine ya jawa Imam Nasir A. Ahmad (Abu Khalil Al-funtuwiy) baki a wajen gabatar da nashi Wa'azin, wato Alaramma Kabir Hussain Daura.
Wa'azin, an gudanar dashi ne karkashin umarnin Shugaban Kungiyar na jiha, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, wanda ya sami halartar Manyan Malaman Kungiyar ta Jiha, Kasa, kai harma da Kasa-da-Kasa.
Daga cikin Malamai da Alarammomin da sukayi Wa'azi a wajen sun hada da;  
1. Sheikh Munir Zango, Daura.
2. Sheikh Mukhtar Zinder.
3. Imam Nasir A. Ahmad Funtua.
4. Alaramma Kabir Hussain Daura.
5. Alaramma Abubakar Maishayi Malumfashi.
Imam Nasir A. Ahmad Funtua, shine mataimakin shugaba na I na Kwamitin Jibwis Social Media na Jihar Katsina, Shugaban Kwamitin Dab'I da Wallafa na Jiha, Babban Limamin Jumu'a a Masallacin Hajarat Plaza dake Funtua, sannan kuma Malami a Jami'ar Al-Qalam dake Katsina. 
Shehin Malamin ya gabatar da nashi Wa'azin ne akan Rukunnan Musulunci a Addinin Shi'a.
Kadan daga cikin wadanda suka sami damar halartar taron sun hada da;
1. Shugaban rundunar Agajin Jibwis ta Jiha, Alhaji N.I. Bakori. 
2. Wakilin Shugaban Kwamitin Da'awa na Kasa, kuma Member a Kwamitin aiyuka na Kasa, Sheikh Abdulbasir Isah Unguwar Maikawo. 
3. Shugaban Kwamitin Jibwis Social Media na Jiha, Malam Muhammad Jameel Maharaz.
Anyi taro lafiya, an tashi lafiya, kuma mun koma gida lafiya.
Domin sauraron yanda wa'azin ya gudana danna wannan link na kasa.

Jim kadan bayan kammala Wa'azin, an gudanar da Meeting na Kwamitin Jibwis Social Media na Jihar ta Katsina karkashin Jagorancin Shugaban nata na Jiha Malam Muhammad Jameel Maharaz Kankara.
An tattauna muhimman abubuwa a wajen taron, kuma In shaa Allahu nan bada dadewa ba za a jimu kuma a ganmu da wasu daga cikin Nasarorin da muka samu damar cimma.
An sanya Wa'azin Jiha na gaba kamar haka:
Gari: Matazu (Yankin Karadua)
Rana: Asabar da Lahadi 11 da 12/03/2017.

Allah yasa muyi tarayya daku a cikin ladan. 

Albany Dabai, 
Jibwis Social Media,
Katsina State.
13/02/2017.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve