Saturday, 5 November 2016

LABARAI A TAKAICE

*Gwamnatin Nigeria ta musanta zarge-zargen cewa tana nuna son kai da siyasa a yaki da cin hanci da rashawa.

*Ministan shari'a na Najeriyar, Barrister Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa duk wanda aka samu da laifin wawure kudin gwamnati za'a gurfanar da shi gaban kuliya.

*Ya kara da cewa babu wata doka da gwamnatin kasar ke karyawa wajen tsarewa da kuma gurfanar da wadanda aka samu da laifin almundahana da cin hanci da rashawa.

*Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da wasu hukumomi domin samar da karin megawat 500 na wutar lantarki a kasar.
Wannan yarjejeniya, kamar yadda mahukunta ke cewa, za ta taimaka wajen bude wa wasu kamfanoni ido wajen zuba-jari a bangaren samar da makamshi a kasar.

*Najeriya ta ce an cimma yarjejeniyar ce da kamfanoni da kuma wasu hukumomi irin su kamfanin samar da wutar lantarki na yankin Niger-Delta, wato Niger Delta Power Holding Company, tare da agajin Bankin Duniya

Kungiyar Hisbah a Jihar Jigawa ta kama sannan ta far-fasa kwalaben giya sama da 200 a garin kazaure , Jihar Jigawa.
Kwamandan Hisbah a jihar Saidu Aliyu ya ce kungiyar ba za ta bari ana aikata ayyukan masha'a ajihar ba.

*Sake matsaya da hukumar shari'a ta Najeriya ta yi da ba da umurnin dakatar da alkalan nan 7 da hukumar tsaron farin kaya ta ke bincike da cin hanci da rashawa, ba za ta rasa nasaba da daukar shawarin kungiyar lauyoyi da ta ba da shawarin ba .

*Ita ma kungiyar lauyoyin tun farko ta ki amincewa da binciken alkalan kafin sake matsaya.

*Hakan na nuna, yarda da matsin lambar kawar da alkalai har sai an kammala bincike da shari'ar su.

*Alkalan dai sun shafi na kotun koli da babbar kotun tarayya.

*Yanzu dai za a jira a ga yadda za a gurfanar da alkalan gaban kotu, ko maganar nan ta Hausawa da ke cewa DAUROWA TA KE A DAURE ALKALI za ta zama gaskiya

*Gidajen man kamafanin fetur na Najeriya "NNPC Mega Stations" sun koma ka'idar karshe ta sayar da fetur a kan lita Naira 145.

*Dama haka ka'idar take tun kara farashin man daga Naira 87 zuwa 145 amma a gidajen man NNPC akwai rangwamen naira 2-3.

*Kakakin kamfanin NNPC Garbadeen Mohammed ya ce dama ba wanda a ka tilastawa ga yadda zai sayar da mai indai bai fi Naira 145 da a ka kaiyade ba.

*A yau ne sarakuna daga ciki da wajen Najeriya za su yi wani kasaitaccen hawan daba a birnin Sakkwato domin taya Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar murnar cika shekaru goma bisa gadon mulki.

HOTO: Sarkin yakin Sarkin Musulmi, Kuma Sarkin Gombe na goma sha daya, Abubakar Dan Usmanu dan Abubakar. "GYARA KIMTSI"

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
05/Safar/1438
05/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve