*Shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai halarci taron kula da lafiyar muhalli da za a gudanar a kasar Morocco a litinin din nan.
*Taron dai wanda majalisar dinkin duniya ke daukar nauyin gudanar da shi zai tabo lamurra na kula da lafiyar muhalli da ke kawo cikas ga malafar duniya "ozone layer" da ke kare duniya daga zafin rana.
*Shugaban na Najeriya zai yi amfani da damar wajen baiyana yadda gwamnatin sa ke aikin tsabtace yankin Ogoni da malalar gurbataccen mai ya yi wa illa .
Hakan dai zai iya jawo tallafi daga manyan kasashen duniya.
*Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Najeriya Abdulmumin Jibrin ya rubutawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wasika da baiyana bukatar goyon baya kan abun da ya ce gwagwarmayar yaki da almundahana ne a majalisar wakilai.
*Jibrin wanda ya ke zaman mafaka a turai don zargin barazana kan rayuwar sa,ya ce zai zo Najeriya duk lokacin da a ke bukatar sa ko a ke tuhumar sa da wani laifi.
*A cewar Jibrin, mara ma sa baya ga wannan aikin na kalubalantar shugabannin majalisar, zai karfafawa wassu nan gaba su dau irin wannan matakin.
*In za a tuna majalisar wakilan ta dakatar da Abdulmumin Jibrin tsawon kwana 180 na majalisa da hakan ya kai tsawon shekara daya.
*Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris na shirin daukar bakuncin taron shugabannin 'yan sanda na Afurka ta yamma don lamuran yaki da cin hanci da rashawa da kuma tsaro.
*Ibrahim Idris wanda ya kai wata ziyarar aiki turai, na ganin kara muhimmancin aiki tare tsakanin kasashe ga lamuran 'yan sanda don nasarar yaki da barayin biro.
*Amurka ta rufe ofishin jakadancin ta a birnin Kabul din Afghanistan do kau da bara ga lamuran hare-hare daga 'yan Taliban.
*Taliban dai ta dauki nauyin kai hari kan wata cibiyar sojan saman Amurka da ke daf da birnin Kabul inda mutum 4 su ka rasa ran su 16 su ka samu raunuka.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
14/Safar/1438
14/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve