Friday, 27 December 2019

FITOWA TA 3.
*Daga Littafin:AUREN MUTU'A A WAJEN YAN SHI'A.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 4.
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*YÃDÃWA:-www.jibwiskatsina.blogspot.com

        Ya zo a wannan littafin har yau,sun dangana ga Annabi(s.a.w) cewa wai yãce: ''Wanda ya yi mutu'a sau zai amince fushin Allah,wanda ya yi mutu'a sau biyu za'a tashe shi tare da zababbun bayi,wanda ya yi mutu'a sau uku zai hada kafada dani a aljanna".
(A duba MAN LA YAHDURUHUL FAKIH na ALKUMMI,muj.na 3 sha.na 336)

A wata ruwayar mai kama da wannan,sun kaga wa manzon Allah(s.a.w) cewa wai ya ce: ''Wanda ya yi mutu'a sau daya zãta zama(gare shi) kamar darajar Husaini(A.s);wanda ya yi Mutu'a sau biyu darajarsa kamar darajar Hassan(A.s) ce;wanda ya yi Mutu'a sau uku darajarsa za ta kasance kamar darajar Ali(A.s);kuma wanda ya yi Mutu'a sau hudu darajarsa kamar darajãta ce".
(Fatahallah kashãni,Tafsiru Minhais Sadikin,bugun Maktabatus Sadar,Tehran-Iran,1379 B.H.,muj.na 2 sha.na 493.)

Da yake mata suna da karin kunya akan maza,watakila za su bukaci a kara dan ingiza su kadan kafin su fada ramin alfasha.Don haka Alkummi wanda suke wa lakabi da Alsaduk (watau mai yawan gaskiya!) ya kitsa musu tãsu ruwaya ta musamman. Ya ce, ''Lokacin da akayi isra'i da Annabi(s.a.w) zuwa sama,ya ce: Jibrilu ya riske ni ya ce:Ya Muhammad,Allah mai girma da daukaka yana cewa :Lallai ni na gafartawa masu yin Mutu'a daga matãyen al'ummarka."
(A duba MAN LA YAHDURUHUL FAKIH,muj na 3 sha.na 463)

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 4 Insha Allah.

Abu Amatullah Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.,

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve