Friday, 8 November 2019

*FITOWA TA 23
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Saboda haka,ko wane abu sãmamme sãmuwarsa ta dogara ne da sãmuwar hanyar sanin sa,gãne shi,koyon sa,ko fahimtar sa.Wannan yana nufin cewa,hanyoyin fahimtar abubuwa da muke dasu (ji da gani da shãqa da dandano da shãfa),su ne suke bai wa abubuwan samuwa,su siffanta su,su tsãra su a cikin kwakwalwa:ido ya ce farare ne ko jãjãye,kanana ne ko manya;hanci ya ce mãsu kamshi ne ko mãsu wãri;baki yace mãsu zãki ne ko mãsu dãci;kunne yace mãsu amo ne ko marasa amo;jiki yace masu taushi ne ko mãsu kaushi;da sauransu.Yãyin da wadannan kafafen fahimta suka gushe,duk wadannan sifofi da tsãre-tsãre sai su gushe:shine Samuwar Ubangiji wacce da ita dukkanin abubuwa suka sãmu.Wadannan samuwa itace a cikin dukkan abinda yake sãmamme,kome girmansa,kome kankantarsa.UBANGIJI YANA CIKIN KOME,SHI NE KOME.

         Wannnan ita ce ainihin ma'anar Dayantakar Samuwa,kuma matakinta shi ne mafi girman matãki da Sufanci ya tãka wanda a cikinsa ya zama tafarki yantacce,kuma ilminsa ya zama ilmi mai zaman kansa.Har yau,a kan wannan matãki ne Sufanci ya yãdu yãduwa mai yawa har ya game duniyar Musulmi bãki daya.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 24 Insha Allah.

          Jibwis Social Media Katsina
              11/Rabi'ul Awwal/1441
                  8/November/2019

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve