FITOWA TA 1.
*Daga Littafin:AUREN MUTU'A A WAJEN YAN SHI'A.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 4.
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*YÃDÃWA:- www.jibwisbirnin-magaji.blogspot.com
بسم الله الرحمن الرحيم
MA'ANAR MUTU'A:AUREN WUCIN GÃDI
Mutu'a,ko kuma auren wucin gãdi,watau auren da ba na dun-dun-dun ba,ma'anarsa shi ne namiji ya kulla jinga da mace cewa zai sãdu da ita sau daya ko sau biyu,ko kuma na tsawon awa daya,ko kwana kaza,ko wata kaza,akan kudi kaza ko lãdan abu kaza.
Auren Mutu'a yana cikin aurace-auracen Jahiliyya kuma anyi aiki dashi a farkon Musulunci kãna daga bisãni aka haramta shi.An karbo ruwãya daga Ali binu Abi Dalib(R.A),cewa "Manzon Allah(S.A.W) ya hana auren Mutu'a da cin naman jakin gida a lokacin (yakin)khaibar.''(Bukhari da Muslim).
Amma yan Shi'a sun ci gaba da halasta Mutu'a kuma sun kãgo ruwayoyin karya wadanda suka nuna falalarta da dumbin ladan wanda ya yi ta,da darajarsa a aljanna.Bãbu shakka sunyi haka domin su bãta al'ummar Musulmi ta hanyar yãda lalata da barna da alfãsha a tsakaninsu kuma don su jãwo hankalin jahilai,musamman matasa,zuwa ga tafarkin su.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 2 Insha Allah.
Abu Amatullah Journalist.
Jibwis Social Media Katsina
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve