Friday, 16 August 2019

*FITOWA TA 13
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI. 
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Allah ya yarda dasu alhali yana sane da abinda yake cikin zukatansu:Ya ce, "Lallai ne,hakika,Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya'a a karkashin itaciyar nan domin ya san abinda ke cikin zukatansu,sai ya saukar da nutsuwa a kansu,kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci.''
(Suratul Fathi:18).
Wadanda suka yi wa Annabi(s.a.w) mubaya'a a karkashin wannan itaciya da Allah ya ambata su dubu da dari hudu ne(1,400).Allah ya ambata cewa ya yarda dasu alhalin yana sane da abinda yake cikin zukatansu,kuma ya kira su muminai.To ta yaya yan shi'a za su ce Sahabban Annabi duka sunyi ridda bayan rasuwarsa wai sai mutum bakwai kawai?

Allah wanda yake ganin abinda yake cikin zukatansu,da ya san za suyi ridda bayan Annabi,ya zai saukar a cikin littafinsa mi tsarki cewa ya yarda dasu?
         Babu shakka maganar Allah ba ta tashi.Shi ya ce ya yarda dasu;su kuma yan shi'a sukace sunyi ridda?
Subhanallah!! Wannan wane irin danyen hukunci ne? Babu Shakka a cikin wannan akwai jayayya da Allah da kuma karyata littafinsa.Allah ya tsare mu da bata.
        "Ya Ubangijinmu! Kada ka karkatar da  zukatanmu bayan har ka shiryar damu,kuma ka ba mu rahama daga gunka.Lalle ne,kai,kai ne mai yawan kyauta.''(Suratu Ãli Imrãna:8).
          "Ya Ubangijinmu,kayi gafara gare mu,kuma ga 'yan uwanmu wadanda suka riga mu yin imani,kada ka sanya kulli a cikin zukatanmu ga wadanda suka yi imani.Ya Ubangijinmu,lalle kai mai tausayi ne,mai jinkai.''
(Suratul Hashri:10).

MUHIMMIYAR SANARWA

     Dukkan littafan malaman shi'a,da muka yi amfani dasu a rubutun wannan takaitaccen littafi,akwai su a dakin karatu(laburare)na cibiyar MARKAZUS SAHABAH dake sakkwato.Laburaren a bude take ga kowa da kowa.
   
Tare da gaisuwar dan uwanku a musulunci.

                   Prof.Umar Labdo.

Abu Amatullah Al-Araby Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve