*FITOWA TA 12
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Allah ya yi gafara a gare su tare da Annabi:
Allah Madaukaki ya ce, "Lallai ne,hakika,Allah ya karbi tubar Annabi da Muhajirina da Ansar wadanda suka bi shi,a cikin sa'ar tsanani,daga bayan zukatan wani bangare daga garesu sun yi kusa su karkata,sa'an nan (Allah) ya karbi tubarsu.Lalle shi ne mai tausayi,mai jin kai gare su.''(Suratut Tauba:117).
Ma'anar ya karbi tubarsu shi ne ya yi musu gafara.To idan Allah ya yi musu gafara,ya wani zai ce sun kafirta ko sun yi ridda ko sun yi zalunci?!!!!
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 13 Insha Allah.
Abu Amatullah Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.,
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve