Saturday, 23 March 2019

Re:

On Mar 22, 2019 8:39 AM, wrote:

*FITOWA TA 11
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

MATSAYIN SAHABBAN ANNABI(S.A.W)
              Sahabban Annabi (S.A.W),Allah ya yarda dasu ,ba su bukatar muyi wani bayani domin kubutar dasu da barrantar dasu daga abinda yan shi'a suka dangana musu na kafirci da ridda da zalunci;saboda babu wani mai da'awar Musulunci da yake shakkar imaninsu,da daukaka,da falalarsu,sai fa wanda Allah ya makantar da basirarsa,ya batar dashi.
           Amma za mu kawo wasu ayoyi na Alkur'ani wadanda suke nuna cewa kudure akidar shi'a dangane da Sahabbai karyatawa ne ga Alkur'ani,kuma karyata Alkur'ani,kamar yadda kowa ya sani kafirci ne.
      ALLAH YA YARDA DA SAHABBAI:
Ubangiji Madaukaki ya ce,"Kuma magabata na farko daga Muhajirina da Ansar da wadanda suka bi su da kyautatawa,Allah ya yarda dasu,su kuma sun yarda dashi,kuma ya yi musu tattalin gidajen Aljanna:koramu suna gudana a karkashinsu,suna madawwama a cikinsu har abada.Wancan ne babban rabo.''
(Suratut Tauba:100).
     To wadanda Allah ya yarda dasu ,ya tanadar musu Aljanna,ta ya za'ace sun kafirta ko sunyi ridda?!!!

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 12 Insha Allah. 

Abu Amatullah Journalist. 
Jibwis Social Media Katsina.,

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve