Tuesday, 5 March 2019

*FITOWA TA 8
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Abinda ya gabata anan dan misali ne kawai na gabar yan shi'a da kiyayyarsu ga zababbun wannan al'umma, watau Sahabban Annabi (S. A. W). Kuma wannan gaba haka take tun ran da makiyin Allah, Abdullahi binu Saba'i Bayahude, ya kafa wannan Kungiya ta Shi'a har zuwa yau. Kuma akan wannan akida ne su ma yan Shi'a na wannan zamani suke. Bari kaji abinda shugabansu kuma babban malaminsu na wannan zamani, watau Ayatullahi Khumaini, yake fadi, Ya zo a cikin littafinsa KASHFUL ASRARI Kamar haka:"Mu anan babu ruwanmu da tsofaffi biyu(yana nufin Abubakar da Umar) da abinda suka aikata na sabawa Alkur'ani, da wasa da sukayi da hukunce - hukuncen Allah, da abinda suka halasta ko suka haramta daga zalunci akan Fadima diyar Annabi (S. A. W), da kuma sauran ya'yansa. Sai dai mu a nan, muna nuni ne zuwa ga jahilcinsu da hukunce-hukuncen Allah da addini.''
(KASHFUL ASRARI, na Ayatullahi Khumaini, 126).
        Duba ka gani, dan uwa mai karatu, Wai Khumaini ne yake dangana jahilci da zalunci ga Sahabban Annabi (S. A. W):Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda!!

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 9 Insha Allah. 

Abu Aisha Journalist. 
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve