*FITOWA TA 10
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Sa'annan daga bisani,ya jefa wa Sahabbai baki dayansu kalmar kafirci.Wal iyazu billah!! Ya ce,"Babu shakka su (Sahabbai) sun baiwa Annabi(s) hakkinsa yadda ya kamata!! (yana yi musu ba'a ne).Annabi wanda ya wahala,ya sha fama,kuma ya jure dukkan musifu domin shiryar dasu,sa'annan ya cika (a lokacin rasuwarsa) alhali yana jin kalmomin Dan Khaddabi wadanda aka gina akan kafirci da zindikanci.''{KASHFUL ASRARI,137}.
Wannan mugunyar akida akanta ne yan shi'ar Nigeriya suke,kamar yadda muka sha ji da kunnuwanmu,kuma muka sha gani da idanunmu,Sai dai sau da yawa sukan boye ta ga mutane saboda TAKIYYA,watau munafurci da yaudara!! Muna rokon Allah Madaukaki ya shirye su,ya arzurta su da kyakkyawar tuba kafin zuwan ajalinsu.Mu kuma,Allah ya shiga tsakanin mu da su,ya tsare mu daga kudure akidarsu.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 11 Insha Allah.
Abu Amatullah Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.,
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve