Monday, 19 March 2018

ZIYARAR GIRMAMAWA GA SHUGABAN JIBWIS NA JAHAR KATSINA SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN

A yau ne Jagororin Daurar Harshen Larabci karkashin Embassy na Kasar Saudiyya da ake gudanarwa a Al-Qalam University ga Daliban illimi suka kawo ma Shugaban JIBWIS na Jahar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautus Sunnah) Ziyarar girmamawa a Gidanshi da ke Katsina.

Yayin da Shugaban Ziyarar Dr. Sufyan Abdallah ke jawabi ya bayyana cewar sun kawo wannan Ziyara ne domin girmamawa ga Sheikh a matsayin shi na Jagoran Da'awah a tafiyar Sunnah a nan Katsina da kuma Kasa Baki Daya. Sannan kuma sun gayyaci Sheikh suna san ya halarci Taron rufewa da za'a gabatar ranar Laraba idan Allah ya Kai mu.

A na shi jawabin Sheikh ya nuna jin dadin shi da irin wannan ziyara da suka kawo ma shi, yayi kuma farin ciki da aka kawo wannan Daurar a Jahar Katsina kuma yayi fatan a dinga gabatar da ita lokaci bayan lokaci.

Sheikh yayi fatan alkhairi yadda aka fara lafiya Allah yasa a gama lafiya‎.

Jagororin sune:

Dr. Sufyanu Abdallah
Dr. Qasmul Bari
Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu
Dr. Aminu Isma'il Kabara

Sun samu rakiyar

Muhammad Jameel Maharaz
Hassan Kabir Yar'adua
Hussaini Kabir Yar'adua

© S.A Media Jibwis Katsina
            01 Rajab, 1439
           19 March, 2018

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve