Tarbiyya Itace Tushen Rayuwa Mai Kyau
Daga Mahmud Isa Yola
Yau a dakin taron kaddamar da shugabanin kungiyar NISA'U SUNNAH reshen jihar Kano, kusan dukkan mahalarta sun zubar da hawayen su a daidai lokacin da 'yar Marigayi Ash-Sheikh Jaafar Mahmud Adam, Malama Zainab Jaafar Mahmud ta ke gabatar da jawabin amincewa da nada ta da kungiyar Izala tayi a matsayar Ameerah.
Babu shakka ba komai masu kuka suke hararowa ba a wannan lokaci illa mahaifin Malama Zainab. Babu shakka rayuwa mafi albarka, mafi kyau, ita ce wacce aka gina ta akan gaskiya da abunda ta kunsa, kuma kowa zai bada shaida bisa kokarin Marigayi Sheikh Jaafar a wannan bangare.
A watannin baya, idan baku manta ba wata wasika ta bayyana wacce Sheikh ya rubutowa malama Zainab, a lokacin ya fita kasar Sudan Karatu, inda a ciki yake gaya mata cewa ya samu damar isowa kasar lafiya... A karshen wasikar, shehin malamin yayi mata wasu kalmomi masu tsada inda yace yana mata "wasiyya da jin tsoron Allah a boye da kuma a fili, da yawan tilawar Al-Qur'ani Maigirma, da sallah akan lokaci..."
Wannan shine wasiyyar malam, wanda a dunkule, shine yana so tayi rayuwa mai kyau, wanda zata yi alfahari da shi a ranar gobe. Kuma babu shakka, ďabbaka wannan wasiyya shine yakai malama matsayin da take.
Wannan abun koyi ne ga matasa, kuma izna ne ga iyaye. A daidai wannan lokaci da galibin mutane suka shagaltu da na'urorin sadarwa na zamani, da yawan bin son zuciya da raunin tunani, babu abunda zai komo da martabar rayuwar mu ta zama mai kyau irin wasiyyar malam na cewa mu ji tsoron Allah, mu tsaida sallah, mu yi karatu tare da aiki da Al-Qur'ani.
Allah SWT Ya gafartawa Sheikh. Allah haskaka kabarin sa, Allah karawa zuriyar da ya bari albarka, Amin.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve