Tuesday, 5 May 2020

SAKON TA'AZIYYA GA YAN'UWA DA IYALAI. DAGA SHUGABAN JIBWIS NA JIHAR KATSINA

SAKON TA'AZIYYA GA YAN'UWA DA IYALAI

Shugaban JIBWIS na Jihar Katsina  Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da yan'uwa da sauran al'umar musulmai bisa rashe rashen yan'uwa da ake tayi a kwanakin nan

Shugaban ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan:

Alh. Malami Usman Ma'aji
(Ma'ajin Kungiyar JIBWIS reshen Jihar Sokoto)
Wanda Allah yayi ma rasuwa ranar 4-9-1441/ 26-4-2020

Alh. Abdulkadir Adamu Jega 
Mai Ladabtarwar Majalisar Agaji ta Kasa, (National Discipline Officer FAG of JIBWIS) 
Wanda yayi ma rasuwa ranar Lahadin da ta gabata

Amb. Dr. Tafida Abubakar Ila Autan Bawo
(Sarkin Rano)
Wanda Allah yayi ma rasuwa ranar Asabar din da ta gabata 2-5-2020

Alhaji Muhammad Ahmad Asha
(Sarkin Kauran Namoda)
Wanda Allah yayi ma rasuwa ranar Lahadin da ta gabata 3-5-2020

Alhaji Iro Sabe
(Kilishin Katsina)
Wanda Allah yayi ma rasuwa yau Talata 5-5-2020

Alhaji Faruk Lawal Bakiyawa
Wanda yan ta'adda suka shiga gidanshi suka kasheshi a daren yau Talata a Garin Bakiyawa

Haka kuma ya na meka sakon ta'aziyyar  ga sauran yan'uwa wadan da suka rasa makusantansu a fadin Jihar Katsina da ma Kasa baki daya

Shugaban JIBWIS Sheikh Sautus Sunnah, ya gabatar da sakon ta'aziyyar ne ga 'yan uwa da iyalan mamatan a Madadin Kungiyar JIBWIS ta Jihar Katsina da yammacin yau Talata yayin da yake gabatar da Tafsirin Ramadan na yau


Muna rokon Allah Ubangiji ya baiwa iyalansu hakuri, ya jikansu, ya gafarta masu, yasa mutuwa hutuce a garesu, tare da sauran wadanda suka rigaye mu, cikin musulmai muminai. Wadan da wannan annoba ta zama silar ajalinsu Allah ya kar6i shahadarsu

Daga karshe yayi addu'ar Allah ya kwaranye mana wannan annoba da ta addabi duniya, ya kawo mana karshenta. Ameen

Yusuf Hassan Buhari
     JIBWIS Katsina
  12 Ramadan, 1441
        5 May, 2020

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve